Gwamnatin kasar Venezuela ta bada sanarwan katse huldar jakadanci da kasar Paraguay saboda goyon bayan ‘yan adawar kasar, wadanda suke riya cewa sune suka lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar yan a shekarar da ta gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran, ta kara da cewa a jiya litinin ce shugaban kasar Venezuela, Nicolas Madoro da kansa ya bada sanarwan katse huldar jakadanci da Asuncion bayan da shugaban Paraguay Santiago Pena, ya shelanta cewa yana goyon bayan shugaban yan adawar kasar ta Venezuela Edmundo Gonzalez a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa wanda aka gudanar a shekarar da ta gabata.
Bayan haka shugaba Pena ma ya bukaci jakadan Paraguay a Caracas ya bar kasar cikin sa’o’i 48 masu zuwa.
Pena ya bayyana haka a shafinsa na Twitter ko X, kan cewa kasar Paraguay za ta yi aiki da sauran kasashen duniya, wajen maida Ganzales kan kujerar shugabancin kasar Venezuela da kuma dawo da tsarin diblomasiyya a kasar.