Shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan ya bayyana anniyarsa ta kyautata dangantaka da kasar Siriya.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka, ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzu dai kasashen Rasha da Iraki ne suke shiga tsakani don tabbatar da cewa dangantaka tsakanin kasashen biyu, makwabtan juna ta koma kamar yadda ake so.
Sai dai gwamnatin kasar Siriya ta sha nanata cewa matukar sojojin kasar Turkiyya sun ci gaba da mamayar wani bangare na arewacin kasar Siriya, to ba zata bude kofar tattaunawa da Turkiyyan ba.
Ta kara dacewa dole ne, da farko Turkiyya ta janye sojojinta daga kasar Siriya da take mamaye da shi kafin a yi maganar tattaunawa da kuma maida hulda da kasar.
Kasar turkiyya dai tana mamaye da wani bangare na arewacin kasar Siriya ne da sunan yaki da kungiyar PKK ta kurdawa yan tawaye wadanda suke sun kafa kasa ta kurdawa zalla a cikin kasar Turkiyya, wadanda kuma suke cikin tsaunukan da ke kan iyakar kasar da kasar Iraki.
Sojojin Turkiya dai suna mamaye da wasu yankuna na arewacin kasar Turkiyya da kuma kasar Iraki tun fiye da shekaru 10 da suka gabata, don yakar yayan kungiyar ta PKK.