Kasar Siriya ta yi kira da a raba yankin Gabas ta Tsakiya da makamin nukiliya
Wakilin dindindin na Siriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ambasada Qusay Al-Dahhak, ya jaddada cewa: Munanan dabi’ar da haramtacciyar kasar Isra’ila ke nunawa, baya ga makaman kare dangi da ta mallaka na nau’o’i daban-daban, musamman makaman nukiliya, na bukatar aiki fiye da kowane lokaci don kubutar da yankin Gabas ta Tsakiya daga wadannan makamai.
A cikin sanarwar da kasar Siriya ta fitar a gaban zama na biyar na taron kafa yankin da ba shi da makaman nukiliya da sauran makaman kare dangi a yankin gabas ta tsakiya, wanda aka gudanar a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York, Ambasada Al-Dahhak ya yi nuni da yanayi mai hatsarin gaske da cewa yankin na ganin yadda haramtacciyar kasar Isra’ila take kaddamar da hare-haren wuce gona da iri, yana mai jaddada cewa dole ne a kawo karshen wannan ta’addanci, da kuma hukunta mahukuntan ‘yan sahayoniyya kan laifukan da suke aikatawa.
Ambasada Al-Dahhak ya bayyana cewa: Yunkurin kafa yankin da ba shi da makaman kare dangi, ba zai iya yin tasiri ba, sai dai idan an dauki matakin dakile barazana mai tsanani da zaman lafiya da tsaron yankin ke fuskanta na rumbunan makaman nukiliya da makaman kare dangi da makare da su, yana mai nuni da cewa: Halayyar ta’addanci ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta hada da nau’ikan makaman kare dangi da take da su, musamman makaman nukiliya, don haka akwai bukatar yin aiki fiye da kowane lokaci na ganin an tsarkake yankin daga makaman nukiliya da duk sauran makaman kare dangi.