Gwamnatin kasar Saliyo ta bukaci jakadan kasar a Guinea ya dawo gida bayan da aka kama wasu mota ta ofishin jakadancin makamare da miyagun kwayoyi wato cocain.
Shafin yanar gizo na labarai na ‘Africa news’ gwamnatin kasar Saliyo ta kira jakadan kasarta a Guinea ya dawo gida, bayanda aka kama wata mota makare da garin Cocain na ofishin jakadancin kasar dauke da akwatuna 7 makare da pawdar kokain,
Ministan harkokin wajen kasar guinea Alhaji Musa Timothy Kabba , yace, Jakada Alhaji Alimamy Bangura wanda baya cikin motar an kirashi don karin bayani, amma an kama wasu daga cikinsu.
Banda haka ministan yace an kama dalar Amurka 2000 a hannun wadanda suke cikin motar, amma sais hi jakadan ya iso zai yi karin bayani kan yadda motar ofishin jakadancin kasar a guinea tana dauke da muggan kwayoyi.