Kasar Libya Ta Bukaci A Kori “Isra’ila” Daga Majalisar Dinkin Duniya

Wakilin kasar Libya a wurin taron MDD akan siyasa da mulkin mallaka,  Ashraf Ali Hamid,ya yi ishara akan manyan laifukan da ‘yan sahayoniya suke aikatawa

Wakilin kasar Libya a wurin taron MDD akan siyasa da mulkin mallaka,  Ashraf Ali Hamid,ya yi ishara akan manyan laifukan da ‘yan sahayoniya suke aikatawa akan Falasdinawa, tare da bayyana wajabcin daukar matakai masu tsauri akan HKI da kuma kawo karshen zamanta memba a MDD.

Wakilin na kasar Libya ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ‘yan sahayoniyar suke yi a Gaza da sauran yankunan Falasdinawa, tare da cewa ya zuwa yanzu sun kashe mutane 44,000, yayin da su ka kuma jikkata wasu dubun dubata.

Bugu da kari Ashraf Ali Hamid ya bayyana cewa da akwai wasu dubun dubatar Falasdinawan da su ka bace, kuma sun rusa muhimman cibiyoyi a Falasdinu.

Ashraf Ali Hamid ya kuma yi kira da a gaggauta kawo karshen laifukan HKI a cikin yankin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments