Kasar Lebanon Ta Yi Asarar Dalar Amurka biliyon 15 A Yakin Da Ta Shiga Da HKI

Ministan tattalin arziki na kasar Lebanon ya bayyana cewa kasarsa ta yi asarar dalar Amurka biliyon 15 sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai

Ministan tattalin arziki na kasar Lebanon ya bayyana cewa kasarsa ta yi asarar dalar Amurka biliyon 15 sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin HKI suka kai kan kasar a yakin watanni 14 da ta shi da kungiyar Hizbullah.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Amin Salam ministan tattalin arziki da kasuwanci na kasar Lebanon, na fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa, asarorin da kasar ta yi sun hada da gidaje kwana, gine-ginen gwamnati, ayyukan ci gaban kasa da kuma wasu asarorin a bangaren tattalin arzikin kasar.

Kafin haka dai Bankin duniya ta bada rahoton cewa, jiragen yakin HKI sun jawo asarori wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka biliyon 8 da miliyon 500 a kasar Lebanon, amma wannan lissafin farko ne.

Sannan ya kara da cewa mafi yawan wuraren da asarar ta shafa dai sun hada da gidajen mutane 99,209 da wasu gine ginen gwamnati da ma na MDD a kasar.

Tun kafin yakin, kasar Lebanon tana fama da matsalolin tattalin arziki tun shekara ta 2019.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments