Jamus ta ba da shawarar yin amfani da dabara mai kyau game da takunkumi kan Siriya
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta bayyana cewa: “Jamus ta ba da shawarar yin amfani da dabara mai kyau da za a gudanar da takunkumin da aka kakabawa kasar Siriya, da haka zai Sanya al’ummar Siriya su samu saukin rayuwa.
Baerbock ta shaidawa manema labarai a birnin Riyadh na kasar Saudiyya a lokacin da take ganawa da ministocin harkokin wajen kasashen yammacin Turai da na larabawa a wani taron shiyya kan kasar Siriya da takwaransu na Siriya As’ad al -Shibani, tana cewa takunkuman da aka kakaba kan Siriya a lokacin shugabancin Bashar Asad kan laifukan tafka laifuka masu hatsari a lokacin yakin basasan kasar, dole ne a ci gaba da gudanar da takunkuman.
Ministar harkokin wajen kasar ta Jamus ta kara da cewa: “Yanzu haka al’ummar Siriya suna bukatar cin moriyarsu cikin gaggawa daga samun canjin Mulki a kasar, kuma kasashen Turai suna ci gaba da taimaka wa wadanda ba su da komai a Siriya, kamar yadda suka yi a tsawon shekarun a cikin yakin basasa a kasar, kuma kasashen Turai za su samar da karin kudi Yuro miliyan 50 na tallafin kayayyakin abinci, mafakar gaggawa da kuma kula da harkar kiwon lafiya.