Ministan harkokin wajen kasar Ireland Michael Martin ya jaddada bukatar kawo karshen yakin Gaza da kuma dakatar da kashe fararen hula da kananan yara cikin gaggawa.
Martin ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: “Suna bukatar ganin an tsagaita bude wuta a Gaza da kuma kara isar da kayayyakin taimakon jin kai ga fararen hula.”
Yana mai jaddada bukatar kawo karshen yakin Gaza cikin gaggawa da kuma dakatar da kisan fararen hula da kananan yara a yankin.
Martin ya bayyana damuwarsa game da rahotanni da suke bayyana irin mummunan harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Asibitin Kamal Adwan tare da janyo rashin aiki a cikinsa sakamakon harin wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila.