Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da shirin gwajin wasu sabbin na’urorin tsaron sararin samaniya a matsayin wani bangare na karfafa matakan sojinta
Kwamandan hedikwatar tsaron sama ta hadin gwiwa a Iran, Qader Rahimzadeh, ya sanar da shirye-shiryen da sojojin Iran suke yi na gwajin wasu sabbin na’urorin tsaron sararin samaniyar kasarsu a lokacin atisayen soji dasuke gudanarwa ba tare da bayyana ko yaushe ba ne a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.
Kwamandan hedikwatar tsaron sama ta hadin gwiwa a Iran ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa: An jibge rundunonin tsaron sama na sojoji da dakarun kare juyin juya halin Musulunci a kusa da wasu wurare masu muhimmanci, tare da jibge na’urori na zamani don kara karfafa matakan kariya.
Ya kara da cewa: Wadannan Dakaru za su gudanar da atisayen hadin gwiwa na tsaro ne a karkashin jagorancin hadaddiyar cibiyar tsaron sararin samaniya ta kasa, a matsayin wani bangare na ayyukan “Karfin Rundunar Sojin Kasa”, da nufin kara karfafa shirinsu na kare sararin samaniyar kasarta Iran.
Ya yi nuni da cewa: Atisayen zata kasance mai dauke da ayyuka masu yawan gaske, amma ba za a ba da cikakken bayani ba saboda dalilan da suka shafi kare sirri da kuma ba da mamakin dabarun yaki ga makiya, wanda kadan ne daga cikinsu za a bayyana ta hanyar kafafen yada labarai.