Kasar Iran Ta Yi Tir Da Harin Ta’addanci Da Aka Kai Kan Masu Ibada A Kasar Siriya

Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta yi tir da harin ta’addanci da aka kai kan masu ibada a masallacin Aliyu bin Abi  talib (As) dake

Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta yi tir da harin ta’addanci da aka kai kan masu ibada a masallacin Aliyu bin Abi  talib (As) dake lardin Homs na kasar Siriya inda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkata wasu na daban a lokacin sallar jumaa.

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il bagha’i da yake bayani game da abin da ya faru ya jaddada matsayin iran na yin Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai kan masu ibada da basu ji ba basu gani ba,

Haka zalika bagha’I yayi kira da a gudanar da bincike tare da ladabtar da wadanda suka aikata wannan danyen aiki na kai hari kan masu ibada a lokacin sallar juma’a, kuma ya daura alhakin dukkan abin da ke faruwa kan gwamnatin kasar ta siriya, daga karshe kuma ya mika ta’aziyya da kuma tausayawa iyalan wadanda harin ya shafa,

Gwamnatin kasar siriya ta bayyana hari a matsayin na ta’addinci kuma ta ce zaa gudanar da bincike, kuma an kwashe mutanen da suka ji rauni zuwa Asibiti don yi musu magani , kungiyar saraya ansaru sunna sun sanar da alhakin kai hari, ta hanyar da sa bama-bamai a cikin masallacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted