Mataimakin ministan harkokin wajen kasar iran kan al’amuran kasa da kasa kazem Gharibabadi ya bayyana cewa kofar iran a bude take kan duk wata tattaunawar diflomasiya ,kuma a lokaci guda a shirye take ta kare kanta daga duk wata barazana,
Da yake hira da gidan talabijin din al-arabiya a daren jiya ya bayyana cewa Tehran ta kammala martanin da za ta bayar game da tsokacinta kan ra’ayoyin bangaren Amurka game da shawarwarin da ta gabatar a birnin newyork, yace iran ba za ta taba canza matsayinta ba ta hanyar masu shiga tsakani bayan an gama tattaunawa
Haka zalika ya jaddada cewa Iran a kowanne lokaci tana maraba da matakin diflomasiya kuma ba ta gazawa wajen gudanar da ko wacce irin tattaunawa da kowane bangare, yace iran a shirye take ta kare kanta