Kasar Gambia Ta Dakatar Da Druruwan Masu Yin Hijira Zuwa Kasashen Turai

Mahukunta a kasar Gambia sun sanar da cewa, sun dakatar da mutane 780 da suke son yin hijira zuwa nahiyar turai ta hanyar tsibirin canary

Mahukunta a kasar Gambia sun sanar da cewa, sun dakatar da mutane 780 da suke son yin hijira zuwa nahiyar turai ta hanyar tsibirin canary na kasar Spain.

Sanarwar ta ce daga cikin wadanda aka dakatar din da tsare su, da akwai wadanda su ka fito daga kasashen Senegal su 233, sai wasu 197 da su ka fito daga ita kanta Gambia din, da kuma wasu 176 daga kasar Guinea, sannan daga kasar Mali mutane 148.

Jami’an tsaron kasar ta Gambia sun sanar da kama mutanan ne, kwanaki kadan bayan da wani karamin jirgin ruwa ya juye da ‘yan hijirar da yake dauke da su a gabar ruwan kasa da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 30.

Bayan da kasashen Murtaniya, Senegal da Moroco, su ka yawaita sa ido akan iyakokinsu na ruwa, masu son shiga cikin kasashen na turai daga Afirka suna bi ta hanyar Gambia, duk da cewa kasar tana da nisa da kasashen na turai.

Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Gambia ya ce; Dole ne mu kara sa ido akan mutanen da suke kokarin shiga cikin nahiyar turai, ta hanyar amfani da Gambia a matsayin Zangon farko.”

Mutanen yammacin Afirka suna kokarin shiga kasashen turai ta hanyar tekun Atlantika, a cikin kananan kwale-kwale. Sai dai da dama daga cikinsu suna rasa rayukansu kafin su isa inda su ka nufa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted