Rahotanni sun nuna cewa china ta fito fili ta soki matakin da Isra’ila ta dauka na fitar da sanarwar Amincewa da yankin Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kai, yace beijin tana adawa da duk wani mataki na rarraba kasar somaliya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar cihna lin Jian ya fadi a lokacin da yake taron manema labarai cewa yankin somali land wani bangare ne na kasar somaliya bisa dokokin majalisar dinkin duniya da kuma karshin dokokin kasa da kasa, don haka china tana goyon bayan kasar Somaliya da hadin kanta kuma tana adawa da duk wani mataki da zai tauye ikon kasar somaliya.
Yace gwamnatin kasar Somaliya ta fitar da sanarwar yin watsi da wannan ikirari da Isra’ila ta yi, haka ita ma kungiyar kasashen musulmi ta OIC da kungiyar kasashen larabawa da kungiyar tarayyar Afrika dukkansu sun yi watsi da sanarwar da kuma bayyanata a matsayin saba doka.
A ranar jumaa ce fira minsitan isra’ila ya sanar a hukumance, amincewa da yankin Somaliland a matsayin kasa mai yanci, kuma ofishin natanyaho yace tuni suka rattaba hannu kan yarjejeniyar yadda zasu kara karfafa dangantaka tsakaninsu.