A yau Litinin ne dai kasar China ta bude rawar soja da bangarori mabanbanta suka shiga, da su ka hada da sojan ruwa, sama da kuma rundunar dake kula da makamai masu linzami.
Kakakin rundunar sojan China na gabashin Kasar, Xi Yi ya ce, manufar wannan atisayen shi ne jan kunne da gargadi ga jagororin da suke tunanin ballewar yankin Taiwan, kuma daukar matakin ya zama wajibi domin kare kadaicin kasar China.
Haka nan kuma kakakin rundunar China ta gabas, ya ce; Dukkanin bangarorin za su yi aiki tare a lokacin atsayen na soja.”
A yayin wannan rawar dajin za a killace yankin Taiwan ta bangarori 5, za kuma a yi amfani da albarusi mai rai tun daga Safiya har zuwa marece.
Sojojin na China sun hana wucewar duk wani jirgin ruwa ta wannan yankin a tsawon lokacin da ake gudanar da rawar dajin.
A nata gefen, ma’aikatar tsaron yankin Taiwan ta sanar a shafinta na X cewa: ita ma ta fara rawar daji domin mayar da martani ga abinda China take yi.
Wannan matakin na China dai ya zo ne, bayan da Amurka ta yanke shawarar sayar wa da yankin na Taiwan makaman da kudinsu sun haura dalar Amurka biliyan 11, da shi ne ciniki mafi girma na makamai a tsakaninsu.
Gwamatin kasar China ta kakaba takunkumai akan wasu kamfanonin Amurka 20 masu kere-kere a fagen tsaro, da kuma wasu manyan shugabanninsu 10. China din ta dauki wannan matakin ne bisa cewa wadannan kamfanonin suna sayarawa da yankin Taiwan makamai.