Kasar Burkina Faso Ta Zargi Shugaban Faransa Da Cin Mutuncin ‘Yan Afirka

Kasar Burkina Faso ta zargi shugaban Faransa da cin mutuncin ‘yan Afirka bisa da’awarsa cewa: ‘Yan Afirka ba mutane ba ne Shugaban Majalisar mulkin sojan

Kasar Burkina Faso ta zargi shugaban Faransa da cin mutuncin ‘yan Afirka bisa da’awarsa cewa: ‘Yan Afirka ba mutane ba ne

Shugaban Majalisar mulkin sojan a kasar Burkina Faso Ibrahim Traore ya bayyana cewa: Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ci mutuncin dukkanin ‘yan Afirka.

Traore ya ce: “Idan ‘yan Afirka suna son yanke dangantaka da wadannan ‘yan mulkin mallaka, lamari ne mai sauki: Dole ne su kawo karshen duk wasu yarjejeniyoyin da suka kulla da ‘yan mulkin mallaka. Idan kuma ba ‘yan Afirka ba su soke yarjejeniyar ba, kawai sun bukaci su rufe sansanonin sojansu ne a cikin kasashensu, to ba su rabu da ala-ka-kai ba.

Shugaba Traore ya jaddada cewa: Macron ga dukkanin ‘yan Afirka ya gudanar da cin mutunci tare da zubar musu da kima da daukakarsu a idon duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments