Kasar Bahrain Tana Kokarin Ganin Ta Maida Huldar Jakadanci Da JMI

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Bahrain ta bada sanarwan cewa tana aiki dare da rana don ganin ta maida huldar jakadanci tsakaninta da JMI. Tashar talanijin

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Bahrain ta bada sanarwan cewa tana aiki dare da rana don ganin ta maida huldar jakadanci tsakaninta da JMI.

Tashar talanijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto ma’aikatar na fadar haka, a wata sanarwan da ta fitar a yau Talata. Ta kuma kara da cewa, ta tsara al-amuranta na kasashen waje ne tare da umurnin Sarki Hamad bin Isa Al Khalifa da kuma jagorancin Firay ministan kasar, sannan yarima mai jiran gadon sarauta na kasar.

Ma’aikatar ta kara da cewa, gwamnatin kasar tana son samar da huldar jakadanci da dukkan kasashe makobta da ita, kuma musulmi tare da sharadin rashin shiga al-amuran cikin gina na kasar.

Daga karshen sanarwar ta kammala da cewa a halin yanzu dai gwamnatin kasar Bahrain ta na aiki kud da kuda da gwamnatin JMI don ganin a sake maida huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu nan ba da dadewa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments