Kasar Afirka Ta Kudu Tana Ci Gaba Da Bibiyar “Isra’ila” A Kotun Duniya Ta Manyan Laifuka

Gwamnatin Afirka Ta Kudu ta sake jaddada azamarta ta bibiyar HKI a kotun duniya ta manyan laifuka akan laifukan kisan kiyashi da ta aikata a

Gwamnatin Afirka Ta Kudu ta sake jaddada azamarta ta bibiyar HKI a kotun duniya ta manyan laifuka akan laifukan kisan kiyashi da ta aikata a Gaza.

Gwamnatin ta Afirka ta kudu, ta kuma yi watsi da duk wani matsin lamba da Amurka yake yi ma ta domin tilasta ma ta, ta ja da baya.

Ministan alakar kasashen waje da aiki tare, Ronald Lamola wanda ya yi Magana da ‘yan jaridar kasar tasa, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi kasar ta janye karar da ta shigar a gaban kotun kasa da kasa ta manyan laifuka.

Haka nan kuma ya ce; Neman yardar Amurka ba shi ne aikin da Afirka ta Kudu ta sanya a gaba ba, abinda yake gabanta shi ne tabbatar da adalci da kuma aiki da dokokin kasa da kasa.”

Lamola wanda yake halartar wani taro na MDD a birnin New york  ya yi ishara da yadda kasarsa take fuskantar matsin lamba kai tsaye daga gwamnatin Amurka, amma duk da haka ba za ta janye ba, yana mai kara da cewa, manufarsu ita ce ganin an hukunta wadanda su ka aikata laifuka akan fararen hula a Gaza.

Lamola ya kuma ce, abinda suke yi ba wasan kwaikwayo ba ne ko siyasa, batu ne da yake da alaka da dokokin kasa da kasa.

A watan  Disamba na 2023 ne dai kasar Afirka Ta Kudu kai karar HKI a gaban kotun kasa da kasa saboda laifukan yakin da take tafkawa akan al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments