A Iran, yau Litinin ne ake kawo karshen rejistar takarar zaben shugaban kasar domin maye gurbin shugaban kasar mai rasuwa Ebrahim Raeisi.
Gomman ‘yan takara ne da suka hada da fitattun ‘yan siyasa da sabbin fuskoki suka gabatar da sunayensu kafin karshen wa’adin rejistan yau Litini.
A ranar 28 ga watan Yuni ne za a gudanar da zaben na gaggawa domin a zabi sabon shugaban kasar da zai maye gurbin Ebrahim Raeisi, wanda ya rasu a wani mummunan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin Iran a ranar 19 ga watan Mayu tare da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian da wasu mukarabansa.
Manyan ‘yan takarar da suka yi rajista yau Litinin domin su tsaya takara su ne shugaban majalisar dokokin kasar, Mohammad Baqer Qalibaf da tsohon mataimakin shugaban kasa Es’haq Jahangiri.
Kafin nan ‘yan takara masu sassaucin ra’ayi da masu ra’ayin rikau da dama ne suka ajiye takararsu ciki harda tsohon kakakin majalisar dokokin kasar Ali Larijani, magajin garin Tehran Alireza Zakani, tsohon babban mai shiga tsakani kan batun nukiliyar Saeed Jalili, tsohon shugaban kasar Mahmoud Ahmadinejad, tsohon gwamnan babban bankin Iran Abdolnaser Hemmati da Mehrdad Bazrpash, ministan kula da hanyoyi da raya birane a halin yanzu.
Sai wasu tsoffin ‘yan majalisar dokoki mata uku : Zohreh Elahian, Hajar Chenarani da Hamideh Zarabadi wadanda suma suka gabatar da sunayensu domin tsayawa takarar shugabancin kasar.
Yanzu majalisar masu kare kundin tsarin mulkin kasar za ta soma tantance ‘yan takarar, daga nan ne hukumar sa ido kan zaben kasar mai wakilai 12 za ta fitar da jerin sunayen ‘yan takara na karshe a ranar 11 ga watan Yuni.
Sannan wadanda aka aminta da takarar tasu za su shafe makonni biyu na yakin neman zabe, sannan su shiga muhawarar da aka shirya yi a gidajen talabijin kafin zaben.