Search
Close this search box.

Kanani: Duniya Ba Za Ta Manta Da Rawar Da Burtaniya Ta Taka Wajen Samar Da Isra’ila Ba

Parstoday – Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran yayin da yake ishara da irin goyon bayan da Birtaniyya ke baiwa gwamnatin sahyoniyawan ya jaddada cewa:

Parstoday – Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran yayin da yake ishara da irin goyon bayan da Birtaniyya ke baiwa gwamnatin sahyoniyawan ya jaddada cewa: Al’ummar wannan yanki da na duniya baki daya ba za su manta da yadda ‘yan Burtaniya suka samar da gwamnatin wariya ta Isra’ila a tsakiyar kasar Falastinu ba.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Nasser Kanani, ya rubuta a cikin wani sako ta shafin sada zumunta na X cewa: Halin mulkin mallaka na tarihi da yunƙurin ci gaba da aiwatar da shi, ya haifar da rarrabuwa da ƙalubale da rikice-rikice a cikin muhimman batutuwan yankin, ciki har da: Batun Falasdinu, wanda wani muhimmin babi ne na manufofin mulkin mallaka na Birtaniya a gabas ta tsakiya.

Kanani ya kara da cewa: Birtaniyya na da hannu a kisan kiyashi, kashe-kashen jama’a da wahala da kuma raba Palasdinawa da ke zaune a zirin Gaza da yammacin gabar kogin Jordan da muhallansu, ta hanyar goyon bayan gwamnatin sahyoniyawan.

Y ace dukkanin matsalolin da al’ummomin yankin gabas ta tsakiya suke fama dasu, hakan na da alaka ne kai tsaye da manufofi na ‘yan mulkin mallaka, wanda a halin yanzu suke aiwatar da shi a kan kasashe ta wata hanya da kuma sabon salo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments