Yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da Isra’ila ta yi wa shahid Haniyya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce: Bai kamata wani mutum ya yi shakku kan hakkin da Iran take da shi na mayar da mummunan martani kan gwamnatin ‘yan ta’adda ta Isra’ila ba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kanani ya bayyana a taron manema labarai a yau Litinin cewa: Wannan danyen aiki na gwamnatin Isra’ila babban manufarsa ita ce haifar da tarzoma da za ta kawo cikas ga duk wani yunkurin zaman lafiya a Falastinu.
Ya ci gaba da cewa: jinin Haniya zai karfafa azamar Palastinawa da sauran masu neman adalci na duniya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar tai ran ya bayyana cewa: Dangane da matakin mayar da martani daga bangaren Iran kan kisan shahid Haniyeh, babu tantama a cikinsa, kuma duk wasu kiraye-kiraye ga Iran na ta kai zuciya nesa ta hakura da hakan, ba zai yi wani amfani ba.
Ya ci gaba da cewa: Wajibi ne duniya ta yi Allah wadai da wannan aika-aika. Ya ce: Mun bi diddigin taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda aka gudanar tare da halartar kasashe masu kujerun dindindin da wadanda ba na dindindin ba, wanda aka sarin kasashen duniya sun yi tir da wannan aika-aikar da gwamnatin sahyoniyawan ta aikata.