Iran ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta ce faransa ba ta da hurimun tsoma baki a harkokin shari’ar kasar.
Nasser Kanaani ya bayyana cewa : Faransa na amfani da salon harshen damo akan kare hakkin bil’adama, misali rashin taka rawar gani a kisan kiyashin da ake yi a zirin Gaza, sannan gwamnatin Faransa ta kasance mafakar ‘yan ta’adda masu adawa da Iran, don haka faransa ba ta da hurumin tsoma baki a cikin hukunce-hukuncen shari’ar Iran. »
Mista Kanaani ya dangane sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar a baya-bayan nan game da ‘yan kasar Faransa guda biyu da ake tsare da su a Iran cewa : “Muna yin Allah wadai da wannan hali na faransa, musamman kan amfani da bayannan karya.
“Mutanen da aka ambata a cikin sanarwar manema labarai na Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa an kama su ne bisa kwararan hujjoji da shaidu kuma gwamnatin Faransa tana da masaniya game da laifukan da suka aikata.
Kakakin diflomasiyyar Iran ya kara da cewa “Ma’aikatar shari’a ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana da ‘yancin kanta kuma tana mutunta hukunce-hukuncen shari’arta.”