Kamfanin “Neptune Oil” wanda shi ne babban mai sayar da man a yankin tsakiyar Afirka, ya sayi man fetur din da matatar mai ta Dangote take tacewa wanda ya kai ton 60,000.
Kamfanin ya ce yanzu haka yana aiki da matatar Dangote din domin tabbatar da yadda zai rika samun mai akai-akai saboda a sami daidaito a farashinsa a kasuwannin yankin na tsakiyar Afirka.
Kamfanin na Dangote yana da shirin fitar da kaso 56% na man fetur din da yake tacewa zuwa kasashen waje, duk da cewa da akwai yiyuwar fuskantar rashin tabbaci na samun danyen man fetur.
A cikin watan Satumba ne dai kamfanin na Dangote ya fara sayar da mansa a cikin gida ta hanyar babban kamfanin man fetur na kasa NNPC.
Kamfanin man fetur na kasar Nigeria ( NNPC) ya dogara ne da shigo da tataccen man fetur daga waje, sai dai bayan bude matatar Dangote a cikin gida yana fatan rage kashe kudaden waje da ake amfani da su wajen shigo da danyen man fetur din.
A cikin watan Oktoba ne dai aka kulla yarjejeniyar musayar danyen man fetur da kuma tatacce a tsakanin kamfanin NNPC da kuma matatar Dangote, ta hanyar amfani da Naira a matsayin ma’aunin cinikin.