Shugaban Majalisar Shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf wanda ya gana da takwaransa na kasar Habasha Tagesse Chafo ya bayyana cewa: Kasashen biyu da suke da alakar diplomasiyya ta tsawon shekaru 70, sun Shata hanyoyin bunkasa alakokin tattalin arziki, siyasa da al’adu.
Haka nan kuma ya ce; kasantuwar kasashen biyu mambobi a cikin kungiyar Bricks yana kara dankon alakar da take tsakaninsu.
Shugaban Majalisar shawarar musuluncin ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya kuma ce; A shekarar da ta gabata na kai ziyarar aiki zuwa Addis Ababa,mun gana da Mr. Tagesse Chafo, inda na gayyace shi ya kawo Ziyara Iran, kuma an yi wannan ziyarar ce dai a lokacin da kasashen biyu suke mambobi na kungiyar Bricks.
Haka nan kuma shugaban Majalisar Shawarar musuluncin ta Iran ya ce; Habasha Babbar kasa ce a cikin nahiyar Afirka, musamman ta fuskar yawan jama’a, kuma ta yi tarayya da kasashen musulmi akan al’adu masu, musamman ma Iran.
Bugu da kari Kalibaf ya ce, alakar kasashen biyu ta fuskokin siyasa da tattalin arziki ta kai tsawon shekaru 70, kuma an Shata manufafofin da ake son cimmawa a wadannan fagagen.
A nashi gefen, shugaban majalisar dokokin kasar Habasha Tagesse Chafo ya ce; Alakar kasashen biyu ta kai shekaru 70, kuma shekaru 60 da su ka gabata, sarkin kasarmu ya kawo Ziyara Iran,a wannan lokacin kuma tawaga mai girma daga Habashan ta sake zuwa Ziyara Iran.