Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Kasar Iran ta karɓi shawarar da kasar Amurka ta gabatar
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatima Mohajirani ta tabbatar da cewa: Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa ya karbi shawara daga gwamnatin Amurka.
Mohajerani ta rubuta a dandalin X a lokacin taro cewa: Ministan Harkokin Wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gabatar da rahoto kan ziyararsa zuwa birnin New York na Amurka da tarurrukan da ya gudanar a can, ciki har da gabatar da hanyar masu shiga tsakani a New York, game da wani tsari da ya bayyana sharuddan Iran na sake bude mashigar tekun Hormuz.
Ta kara da cewa duk da kokarin da makiya ke yi na killace Iran, tawagar Iran ta gudanar da tarurruka da dama da kasashen Turai, kasashen yankin Tekun Farisa da sauran kasashe, ta kara da cewa ana bin hanyar diflomasiyya don share fagen manufofin kasashen waje.
Ta bayyana cewa: Sayyid Araqchi ya sanar da karbar shawarar Amurka.