Wata marubuciya a jaridar “Haaretz” mai suna No’a Limona’ ta wallafa wata kasida dake cewa; gwamnatin Benjamin Netanyahu ta kasa cimma manufofin yakin,sannan kuma tana kai komo a wuri daya akan tattaunawar musayar fursunoni saboda kawai ya cigaba da zama akan kujerar mulki. Haka nan kuma sojoji suna fuskantar tuhuma akan cewa sun kasa cimma manufofin da aka ayyana tun farkon yaki, na murkushe kungiyar Hamas a fagen yaki da kuma hanata ci gaba da tafiyar da mulkin Gaza.
Wannan marubuciyar ta kuma ce; A lokacin da ake yin kisa a Gaza, mun rika kallonsa cikin isgili wani lokacin da farin ciki da shagube, kuma wannan shi ne abinda mu ka yi dangane da makomar Isra’ilawa da aka kiama. Kuma ba mu baki daya ne mu ka fita kan tituna domin neman a sako su, kuma ba mu yi farin ciki da fitowar fursunonin namu zango na farko ba.
Ita kuwa marubuciya a jaridar “The Maker” Sifan klinjil cewa ta yi: Babban hatsarin da ake fuskanta ba wai tsagaita wutar yaki ba, shi ne rashin cimma manufa daga cikin manufofin yakin. Sannan kuma da kin yin furuci da hakan.
Har ila yau, Kilinjil ta ce; Gwamnati da shi kanshi madugunta sun ki su fito fili kai tsaye su ce mun ci kasa. Kuma rashin gudanar da cikakken bincke mai zurfi akan hakan, hatsari ne ga makomar isra’ila a nan gaba.
Ta kuma kara da cewa; Isra’ila tana gab da dandana kudarta akan musayar fursunoni, da kuma shi kanshi yakin. Ta kuma ci gaba da cewa:
“Mun ci kasa wajen kare ‘yan kasarmu a gidajensu, mun ci kasa wajen kare iyakokinmu. Don haka bai kamata wannan asarar da cin kasar su cigaba da zama marayu ba, ya zama wajibi a hukunta shugabannin soja da na hukuma.