Kafafen Watsa Labarun  Amurka  Sun Sake Fitar Da Bayanai Akan Dan Ta’ddar New Orleans

Mahukuntan kasar ta Amurka sun bayyana wanda ya take mutane da mota ya kuma kashe 15 daga cikinsu da cewa sunansa Shamsuddin Jabbar, kuma tsohon

Mahukuntan kasar ta Amurka sun bayyana wanda ya take mutane da mota ya kuma kashe 15 daga cikinsu da cewa sunansa Shamsuddin Jabbar, kuma tsohon sojan Amurka ne.

Bugu da kari bayanan hukumar  bincike ta ‘yan sanda ( FBI) sun bayyana cewa Shamsuddin haifaffen Amurka ne, kuma gabanin ya kai wannan harin ya wallafa sako a shafin yanar gizo cewa ya rungumi akidun kungiyar IS wato Da’esh, an kuma gan shi da tutarta a yayin da ya  kai harin na New Orleans.

Tashar talabijin din CNN ta ambato hukumar bincike ta ‘yansanda tana cewa an sami wani faifan bidiyo da Shamsuddin yake bayyana aniyarsa ta gayyatar danginsa zuwa wata walima domin ya sami damar yi musu kisan kiyashi baki daya. Sai dai kuma daga baya ya ce, ya sauya tunaninsa, ya shiga kungiyar ISIS.

Ita ma jaridar “Times” ta ambaci cewa a cikin faifan bidiyo din da Shamsuddin ya wallafa a shafinsa na Facebook ya sanar da cewa ya shiga kungiyar ISIS.

Shi dai Shamsuddin ya take mutanen da suke bikin sabuwar shekara a New Orleans da mota, sannan kuma ya fito ya da bindiga ya harbe wasu da dama.

Adadin wdanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar wannan harin sun kai 15, yayin da wasu da dama su ka jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments