Dan jiridan kasar Autralia wanda kuma ya samar da shafin wikileaks Julian Assange ya amince da wasu laifuffukan da gwamnatin kasar Amurka take zarginsa da su, a gaban wata kotun Amurka a arewacin tsibirin Mariyana, da ke tsakiyar Tekun Pecific, inda kutun ta yanke masa hukuncin zaman yari, wanda yayi dai dai da lokacinda ya dade a kurkukun kasar Butaniya.
Labarin ya kara da cewa an kai Assange ya gurfana a gaban kotun ne kwanaki biyu bayan a fidda shi daga gidan yari a kasar Burtania.
Sannan kotun ta yanke maka hukunci dai dai da shekarun da yayi a gidan yari a kasar Burtaniya.
Daga nan Assange ya shiga jirgin sama ya koma kasarsa Australia, inda ya hadu da iyalansa bayan rabuwa na shekaru da dama.
Gwamnatin Amurka dai ta bukaci a mika mata dan jaridai mai shekaru 52 a duniya tun shekara ta 2010 bayan ya watsa wasu asiranta masu himmanci wadanda ta daukesu a matsayin barazana ga tsaron kasarta.
Dan jaridar ya sami mafaka a ofishin jakadancin Ekwado a birnin London na wasu shekaru kafin a kama shi a kai shi wani gidan yari a cikin birnin.