Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya sanya hannu a kan wata bukata ta kara yawan jarin JMI a asusun lamuni ta duniya wato IMF .
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa shugaban Pezeshkiyan ya sanya hannu a kan bukatar kara yawan jarin JMI a asusun ne bisa doka ta 123 a cikin kundin tsarin mulkin kasar.
Kafin haka dai majalisar dokokin kasar Iran ta amince da wannan bukatar a ranar Laraba 30 ga watan Oktoban da ya gabata, sannan majalisar kare kundin tsarin mulki kasar ta amince da hakan a ranar Laraba 20 ga watan Nuwamba da muke ciki.
Bayan haka dai ana saran bukatar zata wuce zuwa babban bankin kasar da kuma ma’aikatar al-amuran tattalin arziki na kasar don aiwatar da ita.