JMI Ta Bukaci A Kori HKI Daga Hukuma Mai Kula Da Mata Ta MDD

Wani babban jami’in diblomasiyya na JMI ya yi kira ga hukuma mai kula da al-amuran mata a majalisar wato  ‘United Nations Commission on the Status

Wani babban jami’in diblomasiyya na JMI ya yi kira ga hukuma mai kula da al-amuran mata a majalisar wato  ‘United Nations Commission on the Status of Women (UNCSW), da ta kori HKI daga hukumar saboda kissan mata da yan mata da tayi kuma take ci gaba da hakan, a zirin gaza fiye da shekara guda da ta gabata.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gharibabadi mataimakin ministan harkokin waje a cikin al-amuran Sharia da kuma kasa da kasa yana fadar haka a cikin wasu wasiku mai kama da juna da ya rubutawa babban sakataren MDD Antonio Guterres, shugaban majalisar tattalin arziki na MDD Bob Rae, Shugaban kwamiti mai kula da al-amuran mata na MDD  Abdulaziz M. Alwasil da kuma hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD, wato Volker Turk.

Garib’abadi ya ce ya fadawa wadannan jami’an MDD kan cewa gwamnatin HKI, a fadin hukumomin MDD da dama, daga cikin har da hukuma mai rajin kare hakkin bil’adama a duniya, sun bayyana cewa bai kamata HKI ta ci gaba da zama mamba a cikin wadannan hukumomi ba, tare da abinda take aikatawa a Gaza.

Ya zuwa yanzu dai sojojin HKI sun kashe falasdinawa fiye da 44,000 a yayinda wasu fiye da 104,000 sun ji rauni. A fadin ” United Nations High Commissioner for Human Rights’ ko kuma ‘hukumar kare hakkin bil’adama da MDD’ a ranar 8 ga watan Nuwamban da muke ciki, ‘kimani kashi 70% na wadanda aka kashe a Gaza mata da yara ne.

Rahoton ya kara da cewa sojojin yahudawan sun kashe yaran Gaza kimani dubu 17, sannan wasu 255,000 sun rasa iyayensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments