Rundunar ruwa ta dakarun kare juyin musulunci ta Iran ( IRGC) sun sanar da nutsewar wani katafaren jirign ruwa mai dauke da kwanten 2500 bayan da ya saba dokar wucewa ta mashigar ruwan.
Kamfanin dillancin labarun ” IRNA” ya nakalto majiyar rundunar Ruwan ta IRGC tana cewa; Jirgin Ruwan yana kokarin ratsawa ne ta wata hanya wacce ta sabawa doka, don haka ya ci karo da nakiyar ruwa, da hakan ya yi sanadiyyar fashewarta da kuma tashin gobaya a cikinsa.
Da safiyar yau laraba ne dai wannan lamarin ya faru kamar yadda majiyar IRGC ta bayyana.