Jirgin Ruwa “Madeleine” Dake Son Karya Takunkumin Gaza Yana Ci Gaba Da Tafiya

Jirgin ruwan na “Madeleine” shi ne na 36 a cikin jerin jiragen ruwan ‘yanci da suke son karya takunkumin da aka kakabawa yankin Gaza tun

Jirgin ruwan na “Madeleine” shi ne na 36 a cikin jerin jiragen ruwan ‘yanci da suke son karya takunkumin da aka kakabawa yankin Gaza tun 2007.

A cikin wannan jirgin ruwan da akwai ‘yan gwgawarmaya masu rajin kare hakkin bil’adama su 12 da su ka fito daga kasashe daban-daban, yana kuma dauke da kayan agaji na abinci da magani.

 Jirgin ruwan ya samo sunansa ne daga wata Bafalasdiniya mai suna; Madeleine Kulaib, wacce ita ce macen farko ta Falasdinu da ta kware a sana’ar kama kifi bayan da mahaifinta ya yi shahada a yayin  yakin da HKI ta shelanta akan Gaza a 2023.

Jirgin ruwan na “Madline” ya taso ne daga kasar Italiya, wata daya bayan da jirgin sama maras matuki na HKI ya kai hari akan wani jirin ruwan wanda ya nufi Gaza akan gabar ruwan Malta.

Daga cikin kayan da jirgin ruwan yake dauke da shi a kawai madarar jarirai, shinkafa, da kuma magunguna da injinan tace ruwa. Haka nan kuma yana dauke da gabobin jikin dan’adam na roba na yara, saboda a yi wa yaran Gaza da Isra’ila ta mayar masakai dashe.

Mafi yawancin masu fafutukar dake cikin jirgin sun fito ne daga kasashen turai, kamar Sweeden Jamus da Faransa. Sai kuma wasu daga Holland da Brazil.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments