Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6

Wa jirgin sama na daukar marasa lafiya ya yi hatsari ya kuma fadi a  kan gidajen mutane a kusa da birnin Nairobi babban birnin kasar

Wa jirgin sama na daukar marasa lafiya ya yi hatsari ya kuma fadi a  kan gidajen mutane a kusa da birnin Nairobi babban birnin kasar ta Kenya  a jiya Alhamis.
AMREF Flaying Doctor,  jirgi ne karamin samfurin XLS ya tashi daga tashar jiragen sama na Nairobi da nufin zuwa wasu yankuna a kasar Somaliland ya fadi jim kadan bayan tashinsa.

An ce matukin bai yi korafin ko akwai Malala a cikin jirgin ba, kuma wani wani gargadi sai kawai anji ya fadi.

A halin yanzu dai ba’a san sababin faduwarsa ba, kuma jami’an tsaro basu bada wani bayani har yanzun yawan mutanen da suka rasa rayukansu ba, ku kuma sunaye da kamanin ko matsayin mutanen da suke cikin jirgin ba.

Har’ila yau yansada sun killace wurin sun kuma fara ayyukan ceto kafin su shiga maganar dalilan faduwarsa.

Har’ila yau kungiyar bada agaji ta red Cross ta kasar sun nufi wurin faduwar jirgin wanda yake unguwar  Kiambu wata unguwa a birnin na Nairobi. saboda ayyukan agaji idan akwai bukatar hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments