Ramaphosa da Putin sun tattauna rikicin Ukraine da batutuwan da suka shafi kasashensu

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna batutuwa da dama a wata zantawa ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin. Ofishin shugaban kasar Afirka ta Kudu ya ce, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, shugaban kasar ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan rikicin Ukraine da kuma […]

Australia ta gargadi Isra’ila game da yunkurin mamaye Gaza

A wannan Juma’a ne Australia ta bukaci Isra’ila da ta janye shirinta na mamaye yankin Zirin Gaza, inda ta yi gargadin cewa hakan zai kai ga barkewar matsaloli na jin kai a yankin. Ministar harkokin wajen Australiya Penny Wang a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Australia ta yi kira ga Isra’ila da […]

Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza

Majalisar ministocin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta amince da kudirin firaminista Benjamin Netanyahu na mamaye birnin Gaza, wanda ke zama matakin farko na wani gagarumin farmakin soji da ka iya kaiwa ga mamaye daukacin zirin Gaza, a cewar wani babban jami’in Isra’ila. Matakin ya biyo bayan tattaunawa sama da sa’o’i 10 da aka shafe ana yi […]

Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi

Ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Aragchi ya rubutawa babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC Hussain Ibrahim Taha, da kuma tokwarorinsa na kasashen Saudiya da Turkiya, Faisal bin Farhan da kuma Hakan Fidan wasiku dangane da bukatar kasashen kungiyar su gudanar da taron gaggawa kan abinda ke faruwa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP […]

Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran

A dai dai lokacinda ake shirin juya yin 40 na shahadar Imam Hussain (a) jikan manzon All..(s) Iraniyawa fiye da miliyon 1.2 suka shiga kasar Iraki daga Iran don halattar wannan makokin. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana ncewa hotunan bidiyo na jami’ann tsaro sun bayyana cewa a lardin Ilam wacce ta […]

Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin

Sayyid Abdul-Malik al-Houthi, shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya ja kunnen Amurka da HKI kan kara tada hankali a yankin Asia ta kudu. Kamfanin dillancin labaran IP ya nakalto shugaban yana fadin haka a jiya Alhamis, a lokacinda yake jawabi ga mutanen kasar jawabinsa na mako mako.  Sayyid Huthi ya bayyana cewa kasashen biyu […]

Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah

Kungiyar Hizbullah da Amal na kasar Lebanon sun bayyan amincewar gwamnatin kasar Lebanon wajen kwance damarar kungiyar hizbullah wani abu ne wanda kasashen waje suka fada masu su yi haka, wanda ya yi watsi da diyaucin kasar Lebanon da kuma cikekken iko a kan kasar. Labarin ya kara da cewa shuwagabannin kasar ta Lebanon sun […]

Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6

Wa jirgin sama na daukar marasa lafiya ya yi hatsari ya kuma fadi a  kan gidajen mutane a kusa da birnin Nairobi babban birnin kasar ta Kenya  a jiya Alhamis.AMREF Flaying Doctor,  jirgi ne karamin samfurin XLS ya tashi daga tashar jiragen sama na Nairobi da nufin zuwa wasu yankuna a kasar Somaliland ya fadi […]