Search
Close this search box.

Jiragen Yakin HKI Sun Keta Hurumin Samaniyar Kasar Lebanon Tare Da Kai Hare-hare

A jiya Litinin ne dai jiragen sama na yaki na HKI su ka kutsa cikin sararin samaniyar kasar Lebanon tare da kai hare-hare a ciki

A jiya Litinin ne dai jiragen sama na yaki na HKI su ka kutsa cikin sararin samaniyar kasar Lebanon tare da kai hare-hare a ciki yankunan “Ayta-Sh’aba’ da “Dhalusha.

A gefe daya,kungiyar Hizbullah ta Lebanon ta kai harin ramuwa akan sansanoni da cibiyoyin sojan HKI dake kan iyaka da kuma a can cikin yakin “Harmun”.

Har ila yau mayakan na Hizbullah sun kai wani harin a cibiyar sojan saman HKI dake yankin “Jabalu-Mirun”da “Jabalu- Jarmuq” ta hanayar harba makaman katiusha.

Hare-haren na kungiyar Hizbullah das u ka fara tun a watan Oktoba na 2023, sun lalata cibiyoyin leken asirin HKI dake kan iyaka da kuma haddasa asarar ga cibiyoyin soja da sansanonin yahudawa ‘yan share wuri zauna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments