Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce jiragen yakin HKI sun kai hari a garin “Naqura” dake kudancin Lebanon da safiyar yau Alhamis.
Jiragen yakin na ‘yan sahayoniya sun kai harin ne har sau uku ajere akan wata tsohuwar cibiyar kiwon lafiya dake cikin garin, haka nan kuma akan wasu gudajen mutane da suke a kusa.
Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan asarar rayuka sanadiyyar wadannan hare-haren na’yan sahayoniya.
A shekaran jiya Talata ma dai sojojin na mamaya sun kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beirut hari wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama da kuma jikkata wasu.
Hari na shekaran jiya shi ne irinsa na biyu a cikin unguwar Dhahiya tun bayan tsagaita wutar yaki. Haka nan kuma suna ci gaba da kai wasu hare-haren a kudancin Lebanon daga lokaci zuwa lokaci.
Kungiyar Hizbullah ta yi gargadin cewa, ya zama wajibi ga gwamnatin kasar da ta yi amfani da dukkanin hanyoyin da take da su domin takawa ‘yan sahayoniyar birki, gabanin ita ta dauki matakin da ya dace.