Jaridar Premium time ta Najeriya ta nakalto Jaridar New York Time ta kasar Amurka, na cewa jirgi na farko ya sauka a jihar Borno dake arewa maso gabacin kasar a daren Alhamis da ta gabata. Labarin ya bayyana cewa jirdin yana dauke da makamai da kuma sojoji. Kuma ya sauka ne a birnin Maiduguri babban birnin Jihar.
Labarin ya kara da cewa jirgi na farko ya sauka ne a Abuja dauke da sojoji 100. A ranar Alhamis. Mai magana da yawun rundunar sojojin sama na tarayyar Najeriya Samaila Uba ya ce sojojin Amurka ba zasu shiga yaki da yan ta’adda ba.