Jihad Islami: Masu Gwagwarmaya Ba Zasu Taba Mika Makamansu Ba

Haitham Abulghazalan daya daya cikin shuwagabannin kungiyar Jahadul Islami wacce take fafatawa da HKI a Gaza, ya bayyana cewa ba bu wani soja daga kasashen

Haitham Abulghazalan daya daya cikin shuwagabannin kungiyar Jahadul Islami wacce take fafatawa da HKI a Gaza, ya bayyana cewa ba bu wani soja daga kasashen waje ya isa ya taka yanki gaza da nufin kwance damarar mayaka masu gwagwarmaya.  Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Al-ghazalan yana fadar haka a hirar da ta hada shi ta tasahar talabijan ta Al-Masirah ta kasar Yemen, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Amurka ta kwana da sanin cewa, ba za ta iya kwance damarar kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza ba.

Ya ce, ba wanda ya isa ya yi watsi da samuwar dakarun Hamas a Gaza, ya kuma dora mata wasu su gudanar da harkokin yankin. Hamas da sauran falasdinawa ba zasu taba amincewa da wasu daga waje su gudanar da harkokin gaza ba. Kuma ba za su taba amincewa kasashen wasu, ko waye su su shigar da bakinsu a harkokin cikin giza na yankin gaza ba.

Sai kuma Usama Hamdan shima daya daga cikin shuwagabannin Hamas, ya fadawa tashar talabijin ta Al-Masirah kan cewa, HKI bata muntunta yarjeniyar tsagaita wuta da ta dauka a sharma sheikh ba, banda haka hatta yarjeniyoyin da takulla a fagen kasa da kasa ma bata mutun ta su ba.  Hamdan y ace, a marhala ta biyu na yarjeniyar tsagaita wuta a gaza, kungiyar Hamas zata ba zata amince da duk wani iko daga kasashen waje kan falasdinawa a gaza ba, ba zata kwance damarar mayakanta ba, kuma ba zata amince da shishigin wasu kasashe a cikin al-amuran cikin gida na Falasdinawa ba.  Ya ce , HKI ta kasa kwace makamammu a cikin yaki na tsawon shekaru 2, don haka ba zai yu ta sami haka da ruwan sanyi ba.   Daga karshen Hamdan ya kammala da cewa a halin yanzu sojojin HKI basu fita daga cikin gaza ba, kuma kungiyarsa zata dage kan ficewarsu daga gaza kwata-kwata.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted