Jeremy Corbyn ya kafa sabuwar jam’iyyar siyasa a Burtaniya

A wata hira ta musamman da ya yi da tashar Al Mayadeen, tsohon shugaban jam’iyyar Labour ta Burtaniya Jeremy Corbyn ya sanar da kafa sabuwar

A wata hira ta musamman da ya yi da tashar Al Mayadeen, tsohon shugaban jam’iyyar Labour ta Burtaniya Jeremy Corbyn ya sanar da kafa sabuwar jam’iyyar siyasa tare da fitar da tsare-tsaren farko na jam’iyyar a cikin gida da kuma a mataki na kasa da kasa.

Da yake magana daga Landan, Corbyn ya bayyana wani yunkuri da ya samo asali daga tsarin al’umma da “adalci na zamantakewa a gida da zaman lafiya a kasashen waje,” yayin da ya yi kakkausar suka kan manufofin cikin gida na gwamnatin Burtaniya da rawar da take takawa a cikin rikice-rikicen da ke gudana, musamman a Falasdinu.

Corbyn ya ce shi da abokansa, ciki har da MP Zarah Sultana, sun kafa sabon tsarin jam’iyyar, wanda da farko ake kira  “Jam’iyyar ku” a matsayin taken manufar aiki.

Ya ce sunan na iya canjawa a taron kafa babban kwamitin jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a karshen wannan shekara. “Abin da muka yi shi ne gabatar da tsari, yana lissafta ginshiƙai huɗu: zaman lafiya, ciki har da dakatar da bayar da makamai ga Isra’ila, dakatar da haɗin kai a cikin kisan gillar da ke faruwa”; adalci na tattalin arziki; adalci na zamantakewa, da kula da lamurran muhalli. Ya ce jam’iyyar za ta kasance ta al’umma da dimokuradiyya, tun daga tushe.

Ya bambanta wannan tsarin da tsarin da ke cikin tsohuwar jam’iyyarsa ta Labour da ke a karkashin jagprancin Keir Starmer a halin yanzu. Corbyn ya ce jam’iyyar Labour ta taba kaiwa matsayin  da tana da mambobi 600,000 a lokacin shugabancinsa, amma tun daga lokacin da wasu suka kafa masa karan tsana saboda matsayarsa ta neman yin adalaci a cikin dukkanin lamurra, an samar da dokoki na cikin jam’iyyar da nufin dakile duk wani hankoronsa, har ma da korar mambpbin jam’iyyar saboda ra’ayoyinsu na kashin kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted