Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da mutuwar wani jariri da bai wuce kwanaki 35 da haihuwa ba, saboda sanyi mai tsanani a yankin Gaza.
Sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza wacce cibiyar watsa labarai ta Falasdinawa ta nakalto, ta ce, mutuwar wannan jaririn a jiya Litinin ya kawo adadin kananan yaran da suka rasu saboda sanyi mai tsanani sun karu zuwa 8.
Tun farko, kungiyar Agaji ta (UNRUWA) dake karkashin MDD ta sanar da cewa yaran da suka mutu saboda sanyi sun kai 7.
Cibiyar watsa labarun ta Falasdinawa ta kuma kara da cewa, Jarirai da ba a dade da haihuwa ba, suna mutuwa ne saboda rashin mafaka mai kyau da kuma sanyi mai tsanani a Gaza.
Haka nan kuma ta kara da cewa a halin yanzu, akwai jarirai 7,700 wadanda suke fuskantar barazanar mutuwa saboda sanyi.
Tuni lokacinda hukumar kiwon lafiya ta duniya ( W.H.O ) ta yi Allawadai da abinda sojojin Isra’ila suke yi na lalata cibiyoyin kiwon lafiya da su ka hada da rusa asibitin Kamla Adwan. Falasdinawa ‘yan gudun hijira suke rayuwa a cikin hemomin da aka yi da leda, da kuma yadi, a daidai lokacin da ake ruwan sama kamar da bakin kwarya, ga shi kuma ba su da bargunan lullube jariransu, kuma kasar da suke kwance a kanta ta jike.
Da akwai Falasdinawa miliyan biyu da suke rayuwa a gaza cikin wannan halin..