Masanin harkokin soji na jaridar Ma’ariv ta Isra’ila Avi Ashkenazi ya amince da cewa: Isra’ila na fuskantar matsala ta gaske bayan shafe kusan watanni 22 ana yakin Gaza, yana mai cewa gazawar tsarin siyasar Isra’ila na yanke kwakkwarar shawara da kuduri da suka kamata ya sa Isra’ila ta kai ga daya daga cikin manyan shan kaye a tarihinta, na siyasa da kuma dabaru.”
Avi Ashkenazi, wani manazarcin harkokin soji na jaridar Ma’ariv, ya amince cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fuskantar “matsala ta gaske” bayan shafe kusan watanni 22 na yakin Gaza. Ya kara da cewa, “Rashin iyawar tsarin siyasar Isra’ila na yanke shawara da balagagge da sanin ya kamata, shi ne ya sa Isra’ila ta kai ga daya daga cikin babbar kaye a tarihinta, a siyasance da kuma dabaru.”
Ashkenazi ya jaddada cewa: Babban muhimmin wannan shan kashi shi ne gazawar gwamnatin mamayar Isra’ila wajen cimma manufofin da ta ayyana tun daga ranar farko ta yakin, musamman kwato wadanda aka yi garkuwa da su. Ya kara da cewa; Hakikanin abin da ke faruwa a kasa ya tabbatar da cewa; Har yanzu ‘yan gwagwarmaya suna nan da karfinsu yayin da shugabannin gwamnatin mamayar Isra’ila ke ta yawo a shawarwarin da suke yi da kuma trsanantan sabani a cikin gida.