Daruruwan daliban jami’a sun yi jerin gwano a kan titunan birnin Tokyo fadar mulkin kasar Japan, domin yin Allah wadai da yakin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kan kasar Iran.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, daliban sun yi tar era taken yin tir da Allawadai da Amurka da Isra’ila kan yadda suka kai hari a kan kasar Iran, tare da bayyana hakan a matsayin matakin da ya sabawa dukkanin dokokin kasa da kasa.
Tare da yin kira da a kawo karshen yakin nan take ba tare da wani bata lokaci ba, kamar yadda suka kirayi gwamnatin Japan da taka rawa wajen kawo karshen yakin wanda ya cutar da dukkanin al’ummomin duniya, ta hanyar tashin farashin makamashi a duniya.