Babban mai ba da shawara kan harkokin soji ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, Manjo Janar Yahya Rahim Safavai ya bayyana cewa Mashigar Hormuz wani muhimmin bangare ne na Iran, wanda ya bai wa Jamhuriyar Musulunci cikakken iko kan hanyoyin wucewa ta wannan hanyar ruwa a Tekun Farisa.
“Ikon mulkinmu da kuma yadda muke tafiyar da wannan yankin na ruwa ba da’awa ce ta siyasa ba, hakki ne da ba za a iya musantawa ba,” in ji.
Babban mai ba da shawara ga Jagoran ya yi la’akari da takunkumin da aka sanya a Mashigar Hormuz tun farkon lokacin harin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, a ranar 28 ga Fabrairu.
“Iran ba ta neman kara ta’azzara tashin hankali ba, amma ta dage kan ta yi amfani da ikonta gaba daya.
Lokacin da wannan hanyar ruwa ta zama hanyar jigilar kayan aikin soja da ke barazana ga tsaron kasar Iran kai tsaye, aikin dabarun sojojinmu ne na rufe hanyar,” in ji shi, kafin ya jaddada cewa za a ci gaba da kula da wannan hanyar ruwa har sai Amurka ta É—age takunkumin da ta kakaba wa Iran.
Rundunar sojojin Iran tana hana jiragen ruwa wucewa ta mashigar sai dai idan sun sami izini daga hukumar da ke kula da ita.