Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran janar Muhsin Ridha’i ya wallafa sako a shafinsa na ” X” cewa; Za a mayar da martani akan yakin tattalin arziki ta hanyar bayyana da shelanta yankin da aka haramta shiga cikinsa a cikin ilahirin tekun Pasha.”
Haka nan kuma Muhsin Ridha’i ya ce; An gudanar da bitar siyasar da ake aiki da ita dangane da jiragen Ruwan Amurka da kuma sansanonin sojan Amurka.”
Muhsin Ridha’i ya kuma kara da cewa,sabbin makamai masu linzami na Iran din gargadi ne ga Washington.
Iran dai ta kai hare-hare akan jiragen ruwa na dakon jiragen yaki da kuma wani jirgin yakin na daban. Hare-haren sun dugunzuma Amurka da ya sa ta kai harin ta’addanci akan jiragen dakon main a Iran guda uku.
Jamhuriyar musulunci ta Iran ta bakin jami’anta na siyasa da soja, sun sha nanata cewa matukar Amurkan ba ta kawo karshen killace ta ta ruwa da ta yi ba, to kuma jiragen yakin nata za su fuskanci hare-hare.
Babban sakataren koli na majalisar tsaron kasar Iran Janar Muhsin Ridha’i ya ce harin da Iran din ta kai wa jiragen yakin na Amurka na ruwa,tabbatar da gargadin da ta riga ta yi ne a baya.
Tun a cikin watan febrairu ne dai Amurka da Haramtacciyar kasar Isra’ila su ka shelanta yaki akan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da zumar kifar da tsarinta na musulunci.
Sai dai kuma yanzu bayan gushewar watanni 7 daga fara yakin, Amurka ta sami kanta a cikin tsaka mai wuya, ba ta san mafita daga haramtaccen yaki da ta shelanta akan Iran ba.