Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya bayyana cewa: Kare kasar Iran daga barazana ya dogara ne kan karfafa karfin tsaronta
Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran Manjo Janar Seyyed Abdulrahim Mousavi ya jaddada cewa: Hanya daya tilo ta kare kasar daga fuskantar barazana ita ce ci gaba da dabarun karfafa karfin tsaro.
Manjo Janar Mousavi ya aike da sako ga ministan tsaron kasar Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh a yayin bikin ranar masana’antun tsaro, inda ya taya shi murnar zagayowar ranar, tare da jinjinawa irin nasarorin da masana’antar tsaron kasar Iran ta samu a shekarun baya-bayan nan, wanda ya bayyana a matsayin nasarori masu ma’ana, wadanda sakamakonsu ya bayyana a cikin tsayin dakar kalubalantar gwamnatin yahudawan sahayoniyya da Amurka.