Janar  Brown: Idan HKI Ta Kai Wa Lebanon Yaki Zai Fadada A Yammacin Asiya

Janar Chalse Brown wanda shi ne shugaban rundunar hadin gwiwa ta sojojin Amurka, ya fada a jiya Lahadi cewa; Duk wani hari da Isra’ila za

Janar Chalse Brown wanda shi ne shugaban rundunar hadin gwiwa ta sojojin Amurka, ya fada a jiya Lahadi cewa; Duk wani hari da Isra’ila za ta kai wa Lebanon. Zai haddasa fadadar  rikici da Iran.

Tare da cewa Brown bai tantance nau’in matakin da HKI za ta dauka ba a gaba, sai dai ya riya cewa tana da hakkin kare kanta, yana kuma mai yin gargadin cewa, fada da Lebanon zai fadada rikici a wannan yankin.

Brown ya fada wa ‘yan jarida cewa; kungiyar Hizbullah ta mallaki makamai masu yawa fiye da wadanda harkar Hamas take da su.

Tun bayan farmakin “Guguwar Aqsa ne” ne dai kungiyar Hizbulah ta fara kai hari akan manufofin HKI da suke akan iyaka da kuma cikin Falasdinu dake karkashin mamaya.

Hare-haren na Hizbullah sun haddasa barna mai yawa ga ‘yan sahayoniya musamman a sansanonin sojojinsu da kuma kayansu na leken asiri.

A cikin kwanakin bayan nan dai HKI tana maganar shelanta yaki akan Lebanon, yayin da kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa, a shriye take ta mayar da martani mai karfi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments