Search
Close this search box.

Jam’iyyun Hamayya Na Yahudawa Na Zargin Netanyahu Da Yunkurin Durkusar Da Isra’ila

Shugaban ‘yan Dimokuraɗiyya Yair Golan ya yi kira ga shugabannin jam’iyyun adawa a Isra’ila su gudanar da taron gaggawa domin kawar da gwamnatin Firaminista Benjamin

Shugaban ‘yan Dimokuraɗiyya Yair Golan ya yi kira ga shugabannin jam’iyyun adawa a Isra’ila su gudanar da taron gaggawa domin kawar da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu.

Wani saƙon murya da Golan ya wallafa a shafinsa na X ya ce, “A yau, na tuntuɓi dukkan abokaina a jam’iyyun adawa inda na gaya musu saƙona ƙarara cewa ya kamata mu kama hanya iri ɗaya.”

Ya ƙara da cewa, “Isra’ila tana cikin mawuyacin hali kuma tana durƙushewa a fannin siyasa da fannin tattalin arziki da mu’amala da kundin tsarin mulki.

“Komai yana wargajewa a idanunmu. Dole mu yi aiki tare kuma cikin tsanaki tare da jajircewa.”

Golan ya wallafa saƙon da ya tura wa shugabannin jam’iyyun adawa, da ke cewa: “Muna tsaka da yaƙi, inda aka kwashe kwana 328 ana garkuwa da mutanenmu, kana an raba dubban mutane da gidajensu, sannan tattalin arzikinmu yana durƙushewa, kuma sojojinmu sun kwashe tsawon lokaci suna yaƙi ba tare da samu mafita ba.

“Rashin amincewa da gwamnati da kuma matakan da take yin gaban kanta wajen ɗaukarsu bisa muradunta na siyasa su suka tilasta mana yin wannan yunƙuri.”

Da yake yin martani ga saƙon Golan, shugaban jam’iyyun adawa a Isra’ila Yair Lapid ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa, “Za mu ci gaba da yin aiki da dukkan ‘yan adawa, a fili da kuma a bayan-fage, har sai mun kawar da wannan gwamnati da ta jefa ƙasarmu cikin bala’i.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments