Jami’in Iran ya bayyana cewa: Babu wata tattaunawa da aka yi tsakanin Iran da Amurka game da shirin makamashin nukiliya
Wani jami’in Iran ya tabbatar da cewa: Babu wata tattaunawa da aka yi da Amurka game da shirin makamashin nukiliya na Iran, wanda ke nuna cewa buƙatu da ra’ayoyin Amurka sun saba wa buƙatun Iran, kuma dole ne Amurka ta cika sharuɗɗan Iran kafin a fara duk wata tattaunawa ta makamashin nukiliya.
Jami’in na Iran ya shaida wa kamfanin dillancin Reuters a ranar Laraba cewa: Buƙatun Amurka da ra’ayoyinta game da Shirin makamashin nukiliyar Iran sun saba wa buƙatun Iran.
Babban jami’in na Iran, wanda ke da hannu kai tsaye a tattaunawar kai tsaye da Amurka, ya ƙara da cewa: Kalaman Mataimakin Shugaban Amurka J.D. Vance suna wakiltar ra’ayoyi da buƙatun Amurka, yana mai cewa Amurkawa suna da ‘yancin gabatar da buƙatunsu da ra’ayoyinsu, “amma waɗannan ra’ayoyin sun saba wa buƙatun Iran.”
Ya fayyace cewa: Babu wata tattaunawa da aka yi da Amurka game da shirin makamashin nukiliya na Iran, yana mai jaddada cewa: Dole ne Amurka ta cika sharuɗɗan Iran kafin a fara tattaunawar makamashin nukiliya a tsakaninsu.