Jami’an Yan Sanda A Kasar Iran Sun Sha Alwashin Kama Duk Wani Dan Ta’adda A kasar

Shugaban yan sanda na kasar iran yayi gargadi ga wadanda ke da hannun a tashe tashen hankula da suka faru a baya bayan nan, cewa

Shugaban yan sanda na kasar iran yayi gargadi ga wadanda ke da hannun a tashe tashen hankula da suka faru a baya bayan nan, cewa jamai’an tsaro za su ci gaba da farautarsu har sai sun kama mutum na kasarshe dake da hannu kan ayyukan ta’addanci da akayi.

Janar Ahamadreza radan ya bayyana cewa ya zuwa yanzu an kama mutane da dama a lokacin tarzomar wanda suke da alaka kai tsaye da kungiyoyin leken asiri na kasashen waje kuma an samesu da makuden dalolin Amurka kuma ana basu horo kan yadda za su lalata wurare a cikin garuruwa.

Haka zalika ya kara da cewa sun kama mutane da aka horar da su wajen shirya fina-finai in ji radan kuma an umarcesu da su nuna kamar yan sanda ne suka raunatasu yadda za su yi amfani da shi wajen jan hankalin mutane

Daga karshe ya bayyana gazawar makircin makiya sakamon sa ido da mutanen iran suka yi,  yana mai cewa da zarar jama’a sun fahimci halin ta da tarzoma na masu zanga zanga sai su nisanta kansu da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted