Search
Close this search box.

Jami’an Tsaron Tunusiya Sun Sake Kama Dan Takaran Shugaban Kasar Jim Kadan Bayan Sakinsa  

An sake kama wani dan takarar shugaban kasa a Tunisiya mintuna kadan bayan an sako shi Lauyoyi da tawagar yakin neman zaben dan takarar shugaban

An sake kama wani dan takarar shugaban kasa a Tunisiya mintuna kadan bayan an sako shi

Lauyoyi da tawagar yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar Tunisiya Ayashi Zamal sun ce ‘yan sanda sun sake kama shi ‘yan mintoci kadan bayan an sako shi daga gidan yari bisa hukuncin shari’a.

Mahdi Abdel Jawad, memba a yakin neman zaben Zamal, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa: “Rundunar tsaron Tunusiya ta yi awungaba da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.” Lauyoyin Abdel Sattar Al Masoudi da Dalila Bin Mubarak sun kuma tabbatar da cewa an yi awungaba da Zamal ne bayan an sako shi daga gidan yarin Burj Al Amiri.

Kafin sake kama shi, Kamfanin Dillancin Labaran Tunisiya ta gwamnati ya ruwaito cewa: An saki Zamal dan shekaru 43 a duniya ce kuma an dage shari’ar da ake yi masa har zuwa ranar 19 ga watan Satumba don amsa bukatar masu kare shi.

An kama Zamal ne a ranar Litinin din da ta gabata, bisa zarginsa da hannu wajen yin jabun takardu da suka shafi fayil din takararsa na neman tsayawa takarar shugabancin kasar a ranar 6 ga watan Oktoba mai zuwa, inda zai fafata da shugaban kasar mai barin gado Qais Sa’id da tsohon wakilin majalisar dokokin kasar Zuhair Al-Maghzawi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments