Jami’an Tsaron Pakistan Sun kashe yan kungiyar Taliban Pakistan 19

Gwamnatin kasar Pakistan ta bayyana cewa sojojin kasar sun kashe yayan kungiyar Taliban Pakistan 19. Kamfanin dillancin labaran Sahan ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran

Gwamnatin kasar Pakistan ta bayyana cewa sojojin kasar sun kashe yayan kungiyar Taliban Pakistan 19.

Kamfanin dillancin labaran Sahan ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa, sojojin kasar sun kai sumame a gawayen garin Pishawar inda suka kashe yayan kungiyar Taliban Pakistan har guda 19 a sumame guda biyu. Labarin ya kara da cewa gwamnatin Pakistan ma ta rasa sojojinta guda uku, a fafatawar da suka yi da kungiyar ta Taliban.

Labarin ya kara da cewa kungiyar Taliban Pakisatn ta kulla yarjeniyar dakatar da bude wuta a cikin watan mayun shekara ta 2022 amma zuwa watan decemba na wancan shekarar sun yi watsi da yarjeniyar sun kuma koma ciki fafatawa da jami’an tsaro na kasar ta Pakisatn.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakistan Mumtaz Zahrah Baluch ta bayyana a ranar Alham,is da ta gabata kan  cewa, sojojin sojojin kasar Pakistan suna kaiwa yan Taliban wadanda suke samun goyon bayan Talaban na kasar Afganistan hare-hare ne, inda suke samun mafaka a kan iyakokin kasashen  biyu.

Ta kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Pakistan tana son mu’amala da kasar Afganistan ta kafar diblomasiyyane. Ta sojojin kasar Pakistan suna kai hare-hare kan yan ta’adda wadanda suke kashe jami’an tsaron kasar da kuma mutanen da suke rayuwa a yankin tare da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments